Dan takarar APC na tarayya ya yi batan dabo dan gudun shan kamu.

APC Convention
APC Convention

Dan takarar majalisar wakilai ta tarayya karkashin jam’iyyar APC kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure Dr Aliyi Musa Aliyu, ya yi 6atan dabo dan gudun shan kamu bisa zargin badakalar sama da naira miliyan 13.

Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa wani Rabiu Saidu ne ya kai karar Aliyu, tsohon Darakta Janar na Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ga ofishin ‘yan sandan Dala.

Wata majiya ta shaidawa jaridar Solacebase cewa tuni ‘yan sanda suka kame wani abokinsa mai suna Ghali Ibrahim.

Cikin kunshin takardar karar da wanda abin ya shafa Rabiu Saidu, yace Aliyu tare da Dakta Ghali Ibrahim, sun karbar masa kudi har naira miliyan 13 domin gudanar da kasuwanci kimanin sama da watanni 5, saidai tun daga lokacin ba amo ba labari, kan kokarin mayar masa da kudin bayan kiraye-kiraye da sakonnin waya da ya aika a wayoyinsa na hannu amma duk abin yaci tura.

Wakilinmu ya yi kokarin kiran lambobin wayar Dr. Aliyu tun ranar Asabar din da ta gabata amma har izuwa daren Litinin dinnan layukan wayar ta sa a kashe.

Rahotanni sun nuna cewa duk kokarin da ‘yan sandan suka yi na cafke Dr Aliyu ya ci tura domin ya shafe sama da mako guda kenan an nemesa ko sama-ko-kasa babu labari.

Sai dai wata majiya ta shaidawa Jaridar SOLACEBASE a ranar Litinin cewa rundunar ‘yan sandan shiyyar Dala tace za ta mika kwafin karar zuwa sashin binciken manyan laifuka a ranar Talata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here