Cunkoson ababen hawa ya yi ƙamari a babbar hanyar Kaduna–Abuja, direbobi

images 3

Babbar hanyar Kaduna–Abuja na fama da mummunan cunkoson ababen hawa, inda daruruwan direbobi da fasinjoji suka makale na tsawon awanni ba tare da motsi ba.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa wannan mummunan cunkoso na yawan faruwa lokaci zuwa lokaci, musamman a lokutan bukukuwa, kuma yana jefa matafiya cikin matsananciyar wahala.

Wasu daga cikin fasinjoji sun shafe awanni biyar zuwa shida a kan hanya, alhali tafiyar da aka saba yi cikin kusan awanni biyu da rabi ce kawai.

Rahoton ya nuna cewa cunkoson ya haifar da jinkiri mai tsanani ga masu tafiya tsakanin Kaduna da Abuja, lamarin da ya dagula harkokin sufuri da zirga-zirgar yau da kullum.

Daraktan kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, Malam Ali M. Ali, wanda shi ma ya makale a cikin cunkoson, ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakan gaggawa domin magance matsalar.

Ya kuma bukaci a samar da hanyoyi na dindindin da za su hana sake faruwar irin wannan mummunan yanayi a nan gaba, domin rage wahalhalun da direbobi da fasinjoji ke fuskanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here