Barau zai raba Naira 20,000 ga mutum 10,000 masu ƙaramin ƙarfi a Kano

WhatsApp Image 2025 10 06 at 00.41.38 750x430

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, zai raba Naira 20,000 ga mutum 10,000 daga cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano domin tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Malam Isma’il Mudashir, ya fitar, inda ya bayyana cewa za a fara rabon fom na wannan shiri daga ranar Alhamis, 9 ga Oktoban2025.

An shirya rabon kuɗin ne karkashin gidauniyar Barau I. Jibrin (BIJF), wacce Sanata Barau ya kafa domin gudanar da ayyukan alheri, ciki har da bayar da tallafin karatun digiri ga ɗaliban jihar Kano.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin Sanata Barau wajen taimaka wa marasa galihu da kuma inganta rayuwar jama’a kai tsaye.

Karanta: IBB ya kaddamar da harsashin ginin asibiti a wani kauye na Kano

A cewar sanarwar, mutum 6,500 za su fito daga yankin Kano ta Arewa, inda kowace ƙaramar hukuma 13 za ta samar da mutum 500.

Haka kuma, mutum 112 za su fito daga kowace ƙaramar hukuma da ke cikin yankunan Kano ta Tsakiya da ta Kudu.

An bayyana cewa wannan shiri na daga cikin ayyukan da Sanata Barau ke gudanarwa a fannoni kamar ilimi, lafiya, noma, tsaro da sufuri, tare da mayar da hankali kan ƙarfafa mata da matasa domin haɓaka ci gaban yankin Arewa da ƙasa baki ɗaya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here