Tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) ya kaddamar da ginin sabon asibiti a garin kakanninsa na Kumurya, da ke cikin ƙaramar hukumar Bunkure ta jihar Kano.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a ranar Lahadi, inda tsohon shugaban ya samu wakilcin tsohon shugaban sashen leƙen asirin rundunar tsaro, Birgediya Janar Halliru Akilu (mai ritaya).
Akilu ya bayyana cewa Babangida ba zai taɓa mantawa da garin asalinsa ba, kuma yana da niyyar ci gaba da tallafawa al’ummarsa ta kowane fanni.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa Akilu ya jaddada irin gudunmawar da jihar Kano ta bayar wajen haifar da shahararrun shugabanni kamar Janar Sani Abacha, Janar Murtala Muhammad Ramat, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar da sauransu.
Ya ce Babangida ya aike da godiya ga mutanen yankin bisa addu’o’insu, tare da tabbatar da cewa aikin asibitin zai kammala cikin lokaci.
A nasa bangaren, Sarkin Rano Alhaji Muhammad Isa Umar ya gode wa Babangida bisa kawo wannan muhimmin aiki da zai amfanar da dubban jama’a a yankin.
Ya kuma yaba da rawar da malamin addini Sheikh Ibrahim Khalil ya taka wajen tabbatar da an fara aikin.
Wani mazaunin Kumurya, Malam Salihu, ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba, inda ya roƙi Allah ya saka wa tsohon shugaban ƙasa da alheri, tare da albarkar iyalansa.
Asibitin na Kumurya ana sa ran zai rage wahalar da al’umma ke sha wajen samun ingantaccen magani a yankin.













































