Sanata mai wakiltar ta Kano Arewa, Barau Jibrin, ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar shugabancin majalisar dattawan Najeriya.
Sanatan ya bayyana aniyar tasa ne ya yin da yake ansa tambayoyi daga manema labarai a majalisar dake abuja.
Ya ce zai bayyana aniyar tasa a hukumance nan ba da jimawa ba
Barau dai shine na biyu daga cikin sanatocin da suka kai bantan su a zaben da aka kammala, wa dan da suka bayyana aniyar ta su ta tsayawa takarar shugabancin majalisar.
Sanatan ya bayyan kan sa a matsayin wanda yake da kwarewa, don haka shi ya fi da cewa.
Ya kuma yi watsa da nuna bangaren ci ko addini ya yin zaben shugaban majalisar, inda ya ce a duba kwarewa da kuma can-can ta.












































