Takardun bogi: Kotu ta yi watsi da karar da EFCC ke tuhumar Fani-Kayode

Femi Fani Kayode

Wata kotu a jihar Legos ta wanke tare da
sallamar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, daga tuhumar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ke masa na gabatar da takardun jabu na rashin lafiya.

Mai shari’a Olubunmi Abike-Fadipe ta kotun binciken laifuka na musamman da ke zama a Ikejan jihar Legas, ta wanke tsohon ministan a ranar Talata, 4 ga Fabrairun 2025, yayin da take yanke hukunci kan karar da lauyan sa, Norrison Quakers (SAN) ya shigar.

Mai shari’a Abike-Fadipe ta ce masu gabatar da kara sun gaza kafa hujja a shari’a kan tsohon ministan.

Labari mai alaka: Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin kisa a Kano

Alkalin kotun ya ce Fani-Kayode ba shi da wani zargi da zai amsa saboda masu gabatar da kara sun kasa alakanta shi da laifin.

Alkalin ya ce, “bayanan da aka gabatar a matsayin shaida, ba za a iya amfani da su ba wajen tabbatar da zargin da ake masa”.

“Na yi nazari sosai kan shaidun masu gabatar da kara, kuma ban gano inda wanda ake tuhumar ya aikata laifin da ake zarginsa ba.

Sakamakon haka alkalin kotun ta wanke wanda ake tuhuma tare da sallamar sa bisa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Da yake magana da manema labarai bayan sallamarsa, Fani-Kayode ya ce ya yi matukar farin ciki da ya samu ‘yanci saboda ya shafe shekaru 18 a kotu ana tuhumar sa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here