Babban sojan da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai kan sayar da makamai ga ƴan ta’adda ya samu Afuwar Tinubu

Soldier Soldier

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa Manjo Suleiman Alabi Akubo, wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai saboda sayar da makaman gwamnati sama da dubu bakwai ga ‘yan tawayen yankin Neja Delta, afuwa.

Manjo Akubo mai shekara 62, na daga cikin mutane 175 da suka samu afuwa da rangwamen hukunci bayan amincewar majalisar koli ta kasa kan shawarwarin afuwar shugaban ƙasa.

A cewar sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayon Onanuga, ya fitar a ranar Asabar, Tinubu ya rage wa Akubo hukuncin daga daurin rai da rai zuwa shekaru 20 saboda kyakkyawar hali da nuna nadama.

An kama Akubo a shekara ta 2007 tare da wasu manyan sojoji bisa zargin sayar da makaman gwamnati da ke ajiye a rundunar horar da hafsoshin soja ta ƙasa da ke Jaji, da kuma ajiye makamai na rundunar sojoji a Kaduna.

Karin labari: Soja ya kashe matarsa ya kuma kashe kansa a Jihar Neja

Rahotanni sun nuna cewa makaman da suka haɗa da bindigogi, ƙananan bindigogi da roka sun shiga hannun ƙungiyar ‘yan tawayen Kungiyar ’Yantar da Yankin Neja Delta (MEND).

A watan Nuwamba na 2008, kotun soja da ke Kaduna ƙarƙashin jagorancin Alkalin soja Bala Usara, ta yanke wa Akubo da wasu sojoji biyar hukuncin daurin rai da rai, bisa laifin sayar da makaman gwamnati da aka sace tsakanin shekarar 2000 zuwa 2006, waɗanda kimar su ta kai Naira miliyan 100 a lokacin.

Kotun ta bayyana cewa cikin waɗanda suka sayi makaman akwai Sunny Okah, ɗan’uwan Henry Okah, shugaban ƙungiyar MEND. A shekara ta 2016, ƙungiyar MEND ta ce gwamnatin tarayya ta amince da sake duba hukuncin Akubo da sauran sojojin biyar ƙarƙashin shirin afuwar shugaban ƙasa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here