Ba ma biyan kudin fansa ga ƴan bindiga – Martanin NSA ga El-Rufai 

Nuhu Ribadu (1)

Ofishin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ONSA ya yi watsi da zargin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai yayi a wata hira da yayi da gidan talabijin a baya-bayan nan cewa hukumar ta ONSA tana biyan kudin fansa da kuma karin tallafi ga ‘yan bindiga.

ONSA ya bayyana wadannan ikirari a matsayin “maras tushe” kuma ta bayyana gagarumin ci gaba a yaki da ‘yan bindiga inda ta yaba da bajintar jami’an tsaron Najeriya.

“Manufarmu a koyaushe a bayyane take: muna gargadi game da biyan kudin fansa, kuma muna ci gaba da tarwatsa hanyoyin sadarwar masu laifi ta hanyar daukar mataki mai tsauri,” in ji Zakari Mijinyawa, mai magana da yawun hukumar ta ONSA.

Rashin Tsaro: El-Rufai ya zargi gwamnatin Tinubu da ƙarfafa ayyukan ƴan bindiga

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ONSA ya fayyace cewa gwamnati ba ta taba shiga cikin ayyukan biyan kudin fansa ko cin mutuncin masu laifi ba.

ONSA ta yi nuni da nasarorin da aka samu a jihar Kaduna, inda yankunan Igabi, Birnin Gwari, da Giwa, wadanda a da ke fama da matsalar ‘yan fashi, yanzu ana samun kwanciyar hankali.

Sanarwar ta yi nuni da yadda aka kawar da ko kuma kame fitattun jagororin ‘yan fashi da suka hada da Boderi, Baleri, Sani Yellow Janburos, Buhari, da Boka, da kuma kama shugabannin Ansaru da suka kafa sansanoni a Kaduna kwanakin baya.

Sanarwar ta yi kira da a hada kai a yakin da ake yi da ‘yan bindiga inda ta bayyana shi a matsayin “gwagwarmaya” da ke bukatar goyon bayan dukkan ‘yan Najeriya. “Wannan ba lokaci ba ne na kalaman raba kan jama’a, a’a, a tsaya tsayin daka domin kare al’ummarmu,” in ji Mijinyawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here