Jam’iyyar APC ta umarci tawagar lauyoyinta da su nema hakkinta kan ayyana dan takarar gwamna jam’iyyar NNPP Alhaji Abba Kabiru Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da aka gudanar a ranar 18 ga watan jiya na Maris.
Hakan dai na zuwa ne dai-dai lokacin da jam’iyyar ta bayyana ce duk da cewa dan takararta Nasiru Gawuna ya taya sabon zababben gwamnan murna, amma akasin haka, jam’iyyar APC na da yakinin cewa wannan nasara tasa ta wa dokokin zabe da aka shimfida, lamarin da ya sa jam’iyyar yanke wannan hukunci.
Da yake tabbatar da hakan, mai magana da yawun jam’iyyar ta APC Ahmed Aruwa, ya bayyana cewa jam’iyyar APC shiyyar Kano ba ta amince da sakamakon da INEC ta bayyana ba, wanda ya tabbatar da dan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.
A cewarsa, ayyana wanda ya lashe zaben kamar yadda INEC ta sanar ya saba wa dokokin da suka tsara yadda za a gudanar da zaben baki daya.
Daga nan sai Aruwa ya yi zargin cewa INEC ta saba tanade-tanaden dokokin zabe inda ta ayyana Abba Gida Gida a matsayin zababben gwamna.
Haka kuma, ya bayyana cewa, jam’iyyar shiyyar jihar Kano za ta ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar da ke zamanta a harabar kotuna da ke Miller Road.













































