Rahoton dakatar karasa zaben da bai kammalu ba a Tudun Wada/Doguwa Labari Karya ne

IMG 20230401 WA0114 1 750x430 1
IMG 20230401 WA0114 1 750x430 1

Ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, ta musanta labarin da wata jaridar Internet ta wallafa cewa, Babbar kotun jihar ta dakatar da yin zaben da bai kammala ba a mazabar tarayya ta Tudun Wada da Doguwa.

Da yake karyata labarin tare da bayyana shi a matsayin labarin karya, jami’in hulda da jama’a na hukumar shari’a ta jihar, Baba Jibo Ibrahim a yau Asabar ya shaida wa manema labarai cewa babu irin wannan umarni daga wata kotu a jihar.

Baba Jibo Ibrahim, ya zargi wasu marasa gaskiya da yada labaran karya, sannan kuma ya bukaci ‘yan sanda da su yi bincike tare da kamo masu laifin wadanda ke son haifar da rikici a jihar Kano.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa, Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta sanar da cewa za a gudanar da dukkan zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun dokoki na kasa da na jiha a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu.

Wannan ya hada da mazabar tarayya ta Tudun Wada da Doguwa, a cewar INEC.

Hukumar ta ce ta yanke hukuncin ne bisa tanadin dokar zabe da kuma cewa, “sakamakon zaben da aka yi bitar ya tsaya kamar haka, jam’iyyar ta samu kuri’u APC 39,732 yayin da NNPP da ta samu 34,798 sai kuma PDP da ta samu 7,091.”

Da farko dai an bayyana Alhassan Ado Doguwa na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben amma daga baya hukumar ta mayar da martani a kan cewa zaben bai kammala ba.

Sai dai tashar Freedom Radio ta nesanta kanta daga wallafa labarin dakatar da zaben a shafinta tana mai cewa wasu da ba a kai ga gano su ba ne suka bude shafin boge da sunanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here