Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta fara gudanar da bincike kan zargin fyade da aka yi wa wata jaririya ‘yar watanni 18 tare da kashe wata yarinya ‘yar shekara 13 a jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ya fitar ranar Asabar a Bauchi, ya ce an kama wani mutum mai shekaru 59 a duniya bisa zargin fyaden.
Ya kara da cewa an kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi da hada baki wajen kashe yarinyar mai shekaru 13.
Wakil ya ce mahaifiyar jaririyar mai suna Nenkat Danladi, ita ce ta kai kara ofishin ‘yan sanda na Yelwa tun a ranar 8 ga watan Agusta.
Mahaifiyar ta shaida wa jami’an ‘yan sanda cewa taga wanda ake zargin a kan gadonta tare da ‘yarta da misalin karfe 11:30 na dare.

Wakil ya ce wadda ta shigar da karar ta kuma bayyana wasu mutane biyu da ta ke zargin suna da hannu a bacewar yarinyar.
Ya ce daga baya an kama wadanda ake zargin kuma sun amsa laifinsu.
A cewarsa, yayin da ake yiwa Wanda ake zargi da kisan yarinyar tambayoyi, ya amsa cewa yarinyar da ta bata budurwar sa ce kuma tana dauke da juna biyu wata hudu.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce wanda ake zargin ya kara da cewa ya hada baki ne da mahaifiyar yarinyar da ta bace da kuma wani mutum da shi ne ya dauki yarinyar zuwa Gombe domin a zubar mata da cikin.
Ya ce yayin da suke garin Gombe wata mata ‘yar shekara 50 da ke zaune a unguwar Jekada Fari ta taimaka musu, inda aka yi wa Yarinyar allura da wasu abubuwan da ke haifar da zubewar ciki.
“Daga karshe a kan hanyarsu ta zuwa kauyen Mai’ari da ke daura da karamar hukumar Akku ta Jihar Gombe, wadanda ake zargin su biyu da aka ambata sun shake wuyan Yarinyar, wanda hakan ya sa ta fadi a sume daga bisani Kuma ta mutu.
“Hakazalika, aka kona gawar wadda aka kashe din yadda ba za a iya gane ta ba tare da binne ta a wani kabari mara zurfi a wani daji da ke kusa da karamar hukumar Akku a jihar Gombe.
Ahmed Wakil, ya ce yanzu haka ‘yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, ya kuma ba da tabbacin cewa za su ci gaba da bayyana ci gaban da aka samu yayin da ake gudanar da bincike.













































