An tsare daraktan hukumar kulada kayayyaki na sokoto bisa laifin zamba

PRISON
PRISON

An tsare daraktan hukumar kulada kayayyaki na sokoto bisa laifin zamba

A ranar Laraba da ta gabata ne babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Sokoto ta bayar da umarnin acigaba da tsare daraktan hukumar kulada kayayyaki ta jihar Sokoto Hassan Bello a gidan yari bisa laifin zamba ta naira miliyan 1 da dubu 300.

Mai shari’a Ahmad Mahmud ya bada umarni tsare Hassan bayan wasu rahotannin korafe-korafen damfarar da Mista Bello ya shigar.

Alkalin kotun bayan zaman kotun ya dage sauraren karar har zuwa ranar 4 ga watan Oktoba domin sauraren karar dakuma neman beli.

Lauyan mai shigar da kara na Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati Hanafi Sa’ad ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a watan Agustan na 2021.

Mista Bello daraktan gudanarwa a hukumar, an ce ya karbi kudaden ne daga hannun Aliyu Adamu-tsaki, Yusuf Abubakar da Yahaya Salihu a gaban Dahiru Muhammad a Sokoto.

Hukumar EFCC ta yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya gabatar da takaddun daukar aiki na bogi ga wadanda abin ya shafa.

Lauyan da ake kara Aminu Mustapha, ya shigar da bukatar belin wadanda ake tuhumar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here