Wike da wasu jiga-jigai mabiyan sa basu halarci taron kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ba

Samuel Ortom Nyesom Wike and Seyi Makinde 750x430 1
Samuel Ortom Nyesom Wike and Seyi Makinde 750x430 1

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, da Seyi Makinde na jihar Oyo da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu da Okezie Ikpeazu na jihar Abia wadanda ake kyautata zaton masu biyayya ne ga gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, a ranar Larabar da ta gabata, sun kauracewa taron kaddamar da kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP tare da kaddamar da littafin karrama dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar.

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa wanda a cewar mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa shiyyar Arewa Umar Damagum, anasa waje bai halarci taron ba sakamakon rashin lafiya.

Sauran gwamnonin PDP da aka yi imanin cewa suna biyayya ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar dasuka halarci taron sun hada da: Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, Diri Duoye na jihar Bayelsa da Godwin Obaseki na jihar Edo sauran sune Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa da Darius Ishaku na jihar Taraba; Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom; da Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.

Gwamnan jihar Delta kuma mataimakin dan takarar Atiku, Ifeanyi Okowa, shi ma ya halarci taron.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here