Kwanaki biyu gabanin gudanar da babban zabe, Dan takarar gwamnan jam’iyyar Labour a jihar Adamawa, Dakta Umar Mustapha Muqaddas, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Muqaddas, wanda ya bayyana sauya shekarsa a wani taron manema labarai a Yola, babban birnin jihar ya bukaci magoya bayansa da su zabi APC a ranar Asabar.
Asiwaju Bola Tinubu shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, yayin da Peter Obi ke rike da tutar tsohuwar jam’iyyar Muqaddas.
Muqaddas ya ce ya ruguje dukkan tsarin jam’iyyarsa ta Labour a Adamawa yadda sabuwar jam’iyyarsa za ta amfana.
Ya ce magoya bayansa sun shigo jam’iyyar LP ne da imanin cewa za ta samar da madadin da siyasar Najeriya ke bukata ta hanyar ci gaba, gaskiya, hada kai da hangen nesa.
Ya koka da cewa duk da kokarin da suke yi da kyakkyawar niyya, sun gane cewa ba za su je ko’ina ba a kasa da jiha da tsarin da kungiyar yakin neman zaben Peter Obi ta kafa.













































