Shugaban kasa Buhari ya isa katsina gabanin zabe ranar Asabar

Buhari returns back 750x430 1
Buhari returns back 750x430 1

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Katsina inda daga nan ne zai zarce zuwa Daura, mahaifarsa domin halartar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi a ranar Asabar.

Tawagar shugaban kasar ta sauka a filin jirgin saman umar musa yaradua da misalin karfe 4:40 na yammacin ranar Alhamis 23 ga watan Fabrairu 2023.

A ranar Asabar ne ake sa ran zai kada kuri’arsa ga ‘yan takarar da yake so a Daura.

Kafin ya bar Abuja zuwa Katsina, Buhari ya kira taron majalisar tsaro, inda ya gana da shugabannin hukumomin tsaro domin tunkarar su kan batun kare masu zabe da kuma tabbatar da cewa zaben ya gudana.

Buhari ya kuma gana da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu a Abuja, inda ya gargade shi da ya tabbatar an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.

A wajen taron, Buhari ya umarci dukkan ‘yan takarar da suka fafata a zaben da su amince da sakamakon zaben a matsayin zabin masu zabe.

Buhari ya zama shugaban kasa ne a shekarar 2015 bayan ya kayar da magabacinsa, Goodluck Jonathan a zabe mai cike da rudani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here