Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana goyon bayansa ga Atiku

Atiku Abubakar and Dahiru Bauchi
Atiku Abubakar and Dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya amince da zaɓen dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaben da za a yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Ya bayyana cewa ya yanke shawarar goyon bayan Atiku ne saboda yawancin mabiyansa sun amince za su zabi tsohon mataimakin shugaban kasar.

“Ya ku al’ummar Najeriya, zabe ya sake zagayo wa, kuma mabiya na da ke siyasa sun ce za su zabi Atiku.

“Kuma tunda sun ce za su zabe shi, ba zan iya raba hanya da su ba. Ina tare da su. Bari mu ga abin da Allah zai buɗe mana. Allah ya kara mana lafiya, ya kuma kara kare mana kasarmu.

Babban Malamin ya koka da yadda gwamnati mai ci ba ta yi wa kasar nan komai ba, inda ya ce ba daidai ba ne wani ya ce zai ci gaba daga inda gwamnatin ta tsaya.

Ya ƙara da karanto hadisi cewa ba a saran mumini sau biyu a rami ɗaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here