APC ta dakatar da shugaban ta na shiyyar Arewa maso Gabas

Mustapha Salihu Vice Chairman APC NorthEast
Mustapha Salihu Vice Chairman APC NorthEast

Kasa da mako guda a gudanar da zabuka, Jam’iyyar APC ta sanar da dakatar da mataimakin shugabanta na kasa, shiyyar Arewa-maso-Gabas Mustapha Salihu, bisa zarginsa da aikata laifukan yin zagon kasa ga jam’iyyar kwanaki biyar kacal kafin zaben shugaban kasa na 2023.

Haka kuma an dakatar da shugaban jam’iyyar na mazabar Rumde Abdulkadir Abdullahi.

An bayyana dakatar da ‘yan biyun ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Rumde Ward, Abdulhadi Ahmed, da Sakatare, Garba Mohammed da wasu shuwagabanni 16.

A halin da ake ciki kuma, dakatarwar da aka yi wa shugabannin biyu a matakin Unguwa an ce an mika shi ga mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na jihar Adamawa da kuma shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Yola ta Arewa.

Wasikar dakatarwar Salihu ta ce: “Kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC, reshen karamar hukumar Yola ta Arewa sun gudanar da taron gaggawa a ranar Lahadi 19 ga Fabrairu, 2023 tare da la’akari da wasu abubuwa da dama da ke gabanta, tareda dakatar da Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na gabas, Kwamared Mustapha Salihu, kan fallasa ayyukan jamiyyar.

“Saboda haka, bisa bin ka’idojin da suka dace na kundin tsarin mulkin babbar jam’iyyarmu, mambobin kwamitin aiki sun amince da dakatar da Comrade. Mustapha Salihu na tsawon watanni shida da gaggawa ta yadda zai zama abin hana wasu a gaba.

“Yayin da muke godiya ga kwamitin Aiki na jam’iyyarmu na jiha bisa ci gaba da goyon bayan ku, muna fatan shawararmu za ta sami amincewar gaggawa”

Sai dai kwamitin ayyuka na kasa karkashin jagorancin Oshiomole na jam’iyyar APC a shekarar 2018, ya yi fatali da dakatarwar da aka yi wa Mustapha Saliu, inda ya ce “muna bayyana karara cewa dakatarwar da aka yi ta banza ce saboda ofishin shiyyar Arewa maso Gabas ba shi da irin wannan hurumin dakatar da dan kasa. ma’aikaci.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here