Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, a yau Litinin ya tabbatarwa da gidan TV na channels faruwar lamarin.
Inda ya ce masu zanga zangar sun kai wa bankin Keystone, Union da First Bank hari a ranar Litinin.
Ya kuma kara da cewa yanzu haka an kai jami’an yan sanda yakin damun tabbatar da zaman lafiy.
A ranar Alhamis ne dai da ta gabata shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanarwa da ƴan Najeriya cewa tsofaffin takardun kuɗin N500 da N1000 sun daina aiki.
Sai dai shugaban ya ƙara wa’adin amfani da tsohuwar takardar kuɗi ta N200 har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023.













































