Masu kutse daga ketare na kai hari kan bayananmu na sirri – INEC

INEC Mahmood
INEC Mahmood

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce ana ta samun yunƙurin kutse ga tsarin kwamfutocin hukumar lokacin da zaben 2023 ke fuskantowa.

Yakubu ya bayyana haka a ranar alhamis yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja, wanda aka yi wa take “Zaɓen 2023″ shari’a tare da tabbatar da dimokradiyya mai dorewa”.

Shugaban wanda mataimakin daraktan kula da fasahar zamani Dr Lawrence Bayode ya ce hare-haren da ake fuskanta ana samunsu ne daga sassa daban-daban na duniya ba iya Najeriya ba.

“Muna cikin duba kwamfutocinmu jiya, sai kawai muka ga wasu mutane daga Faransa na neman yi mana kutse, amma nan take muka ɗauki mataki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here