Daga Aminu bala madobi.
Bayan shan artabu na kusan sa’o’i da masu safarar makaman da ake zargin sun ɗauko makaman tun daga jihar Taraba domin kai su sansanin ‘yan ta’adda a Zamfara.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar
‘yan sandan jihar SP Mohammed Shehu Anipr, ya sanyawa hannu, ya ce lamarin ya faru ne bayan da jami’an nasu suka samu bayanan sirri game da mutanen dake cikin mota ƙirar ‘Toyota Corolla’ ɗauke da muggan makamai domin kai su sansanin ‘yan ta’adda a jihar.

Bayan musayar wutar ‘yan sandan sun kama mutum biyu waɗanda suka ji munanan raunuka yayin da wasu suka tsere da raunikan harbi a jikinsu.

Kwamishinan yan sandan jihar CP Kolo Yusuf ya sake jadadda burin rundunar na fatattakar yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka daga jihar domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.












































