‘Yar Wazirin Bauchi ta yi murabus daga Kwamishina bayan gwamna ya tube rawanin mahaifinta

Saadatu Kirfi
Saadatu Kirfi

Hajiya Sa’adatu Bello Kirfi, kwamishinan Gama Kai da Kananana Masana’antu na jihar Bauchi ta yi murabus daga mukaminta.

Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan jihar Bauchi ya kori mahaifinta, Alhaji Bello Kirfi daga sarautarsa na Wazirin Bauchi.

Wasikar da sakataren masarautar Bauchi ya rattaba wa hannu ta ce an tsige Kirfi ne daga mukaminsa kan ‘rashin biyayya da girmama gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.

A wasikarta mai dauke da kwanan wata na 4 ga watan Janairu, Sa’adatu ta yi godiya ga gwamna bisa bata damar aiki a gwamnatinsa, amma bata bayyana dalilin murabus din ba.

“Mai girma, ina son mika murabus dina a matsayin mamba ta majalisar zartarwa na jihar Bauchi da kwamishina ta ma’aikatar Gama Kai da Kananana Masana’antu na jihar Bauchi nan take.

“Ina son gode wa mai girma gwamna bisa damar da ya bani na yin aiki a karkashin gwamnatinsa.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here