Sojoji sun yi luguden wuta kan kasurgumin kwamandan boko haram

NAF airstrikes
NAF airstrikes

Bayan tsallake rijiya da baya daga hare-haren da sojojin Najeriya ke kai wa, wani shararren shugaban kungiyar Boko Haram Abou Hurairah, ya kwanta dama.

PRNigeria ta rawaito cewa an hallaka Abou Hurairah tare da wasu kwamandojin Boko Haram a hare hare ta sama da sojojin sama suka kaddamar.

Hakan na zuwa ne biyo bayan wani harin bama-bamai da Rundunar Sojojin Sama na Operation Hadin Kai suka yi, ta hanyar amfani da jirage masu saukar ungulu guda biyu na rundunar sojojin saman Najeriya.

Abou Hurairah, da sauran jiga-jigan ‘yan Boko Haram da aka kashe, su ne ke kai hare-hare a Mahadar monguno na Jihar Borno a kwanan nan.

Wata majiyar leken asiri ta tsaro ta shaidawa PRNigeria cewa, Abou Hurairah da sauran kwamandojin ‘yan ta’adda ne ke hada kai da kuma ba da umarni ga sojojin da ke sanar da su wajen kai hare-hare kan al’ummomi daban-daban a cikin Monguno da sauran yankunan Arewa maso Gabas a Borno.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here