Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun dakile wani harin‘ yan bindiga tare da kashe wani shahararren dan fashi a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da safiyar Alhamis.
ASP. Mohammed Jalige, jami’in hulda da jama’a na rundunar ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai karin haske a Kaduna.
“Da misalin karfe 7 na safe rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 5:45 na asuba cewa wasu‘ yan bindiga da yawa sun tare babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja kusa da wata gada da ke kan kauyen Kasarami suna harbin masu ababen hawa.
“Nan take rundunar ta tara ma’aikatan runduna ta musamman ta (Operation Puff Adder I) a Rijana kuma sun yi artabu da‘ yan bindigar.
Karanta Wannan: DA DUMI-DUMI: Femi Fani Kayode Ya Fice Daga PDP Zuwa APC
“Wannan ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin‘ yan fashin yayin da wasu suka shiga daji da raunuka daban -daban na bindiga.
“Saidai labara mara dadi shine wani direban motar haya lambar Lagos KDR 602 XF da kwandastan sa sun gamu da ajalinsu, ”inji shi.
Kakakin rundunar ya ce za a ba da bayanin gawar dan fashin, yayin da aka ajiye gawawwakin direbobinn a asibitin St. Gerald da ke Kakuri Kaduna.
Karanta Wannan:YANZU-YANZU:Shugaban Hukumar EFCC, Abdurrasheed Bawa, Ya Yanke Jiki Ya Faɗi
Ya yi kira ga mazauna yankin da su rika ba jami’an tsaro bayanai masu mahimmanci a kan lokaci domin daukar matakin gaggawa. (NAN)










































