Sama da hukumomi 100 ne ke kan siradin samun ragi a kasafin kudin 2023 – Majalisar dattawa

Senate
Senate

Majalisar dattijai ta ce akwai yiwuwara rage kasafin kudin 2023 na wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati sama da 100, wadanda suka gaza kare kudaden dasuka kashe tsakanin 2017-2022.

Shugaban majalisar dattijai Dr Ahmad Lawan ya bayyana haka yayin da yake mayar da martani ga wani batu da Sanata Mathew Urhohide (PDP-Edo) ya bayar a kan yadda hukumomi keyin watsi da gayyatar da kwamitin majalisar dattijai kan asusun gwamnati suka yi masa na bayyana kudaden da suka kashe.

Lawan ya ce duk wani jami’in gwamnati da ya yi amfani da kudaden jama’a dole ne ya kasance cikin shiri don bajakolin yadda yadda kashe kudaden “Kuma duk wani jami’in da yake ganin ya fi karfin doka ya yi murabus.

“Za mu ba su lokaci su bayyana, kuma idan sun kasa bayyana kafin mu zartar da kasafin kudin, mun yanke kasafin su na 2023.

Sen.Mathew Urhohide (PDP-Edo) wanda ya gabatar da kudirin, bayan da ya bayar da misali da tsari na 42 da 95 na dokokin majalisar dattawa, ya ce majalisar ta baiwa kwamitin asusun gwamnati ikon duba ayyukan hukumomi ta hanyar yin kira ga jami’an asusun ajiyar su da su yi lissafin kudaden da suka kashe.

A cewarsa, akwai wasu hukumomi da suka ki bayyana a gaban kwamitin domin yin bayani kan abin da suka kashe.

Wasu daga cikin hukumomun da suka gaza bayyana gaban Kwamitin sun hada da:

Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Ofishin Kasafin Kudi na Tarayya, Kamfanin Kasuwancin Lantarki na Najeriya Plc, Ma’aikatar Harkokin Waje, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa.

Sauran sun hada da hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure, ma’aikatar tsaro, sojojin saman Najeriya da ofishin mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin Neja Delta da dai sauran su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here