Kotu ta soke takarar Binani a matsayin ‘yar takarar Gwamna a Jam’iyar APC ta adamawa

Senator Aishatu Dahiru Binani
Senator Aishatu Dahiru Binani

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Yola a ranar Juma’a ta soke zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da ya tsayar da Sanata Aishatu Binani a matsayin ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa.

A wani hukunci da mai shari’a Abdulaziz Anka ya zartas ayau Juma’a, kotun ta bayyana cewa an yanke hukuncin ne bisa dogaro da wasu kwararan hujjoji na rashin bin ka’idojin jam’iyya da na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.

Nuhu Ribadu wanda ya zo na biyu a yayin zaben fidda gwanin ne ya maka Binani, APC, da hukumar zabe INEC gaban babbar kotu, inda yake neman a soke zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayun 2022.

Ya nemi a haramtawa Sanata Binani tsayawa takara bisa zargin saye kuri’un wakilan deleget ba bisa ka’ida ba daga karamar hukumar Lamurde ta jihar.

Kotun ta bayyana cewa babu dan takarar jam’iyyar APC a jihar a zaben 2023, sai dai kotun ta ce mai kara da wadanda ake kara suna da damar daukaka kara kan wannan hukuncin.

A nasa martani, Nuhu Ribadu da Sanata Binani sun ce zasuyi nazari kan wannan hukuncin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here