Dan takarar gwamna na jam’iyyar ADP kuma dan majalisar wakilai na mazabar Kano Municipal Hon. Shaaban Ibrahim Sharada ya taya Barista Aisha Dankani murnar cika shekaru 60 da haihuwa.
Dan takarar ya bayyana hakan ne acikin wata sanarwa da kwamitin yakin neman zaben sa na gwamna ta fitar mai dauke da sa hannun kakakinsa Abbas Yushau Yusuf a karshen mako.
‘’Sharada ya bayyana Hajiya A’isha Dankani a matsayin mace ta kwarai kuma mai kwazo a tsakanin matan Najeriya.
Ya ce Aishar wata kadara mai tsada wadda take taka rawar gani a kungiyoyi masu zaman kan su da na gwamnati wajen ciyar da Kano da Najeriya gaba,” in ji sanarwar.
‘’Hajiya A’isha Dankani wacce a halin yanzu ita ce ‘yar takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar ADP a Kano, ta cancanci a taya ta murna saboda yadda take cudanya a ma’aikatun gwamnatin tarayya da kungiyoyi daban-daban dan ci gaban Majalisar Dinkin Duniy. Ta kuma kasance Darakta a hukumomin gwamnatin tarayya kuma ta kasance Sakatare na dindindin.
“Babu shakka, Barrister wata babbar jigo ce ta cika shekaru sittin, ta sadaukar da ita bisa tallafawa fasahar kere-kere da Kano da Najeriya tun bayan kammala karatunta a shekarar 1985 a Kwalejin Shari’a ta Jami’ar Bayero Kano. Ta kuma yi aiki a matsayin Mai sharia, Darakta a Fadar shugaban kasa, Ma’aikatar Harkokin Mata, Sashen bincike na Tsare-tsare da kididdiga da sauransu.
“A madadin kaina, da iyalina, al’ummar mazabar karamar hukumar birni da daukacin magoya bayan jam’iyyar ADP na taya Barista Dankani, MFR, mni murnar cika shekaru sittin na hidimtawa jama’a.”
‘Dan takarar Gwamnan Kano yace idan ADP ta samu nasarar mulki a 2023, Hajiya Aisha Dankani a matsayin Sanata, za ta aiwatar da ingantattun tsare-tsare a kan mata da yara da sauran al’amuran ci gaba za su kasance a sahun gaba a manufofin gwamnatinsa.’’












































