Gwamnatin tarayya ta amince a kashe Naira Milyan Dubu 27 Don aikin titin Kishi-Kaiama

BUHARI signs signs 750x430 1
BUHARI signs signs 750x430 1

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara ya ce Gwamnatin tarayya ta amince da gina hanyar Kishi zuwa Kaiama akan kudi Naira Milyan Dubu 27.

Gwamna AbdulRazaq ya ce irin cigaban da aka samu a Abuja ya bayyana amatsayin dalilin da ya sa a yanzu gwamnatin jihar ta dakatar da ayyukan da ta ke yi a kan hanyar.

Jihar kwara ta dauki nauyin gina hanyoyi don saukaka kalubalen sufuri a kan tituna masu yawan cunkoso.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Mista Rafiu Ajakaye ya fitar a Ilori.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bada labarin cewa, AbdulRazaq ya sanar da hakan ne a Ilorin a taron koli karon farko na tattalin arziki da ci gaban jihar wanda kungiyar ci gaban Kwara ta arewa ta shirya.

“Akwai gibin ababen more rayuwa a fadin Najeriya, inda hakan yafi tsamari musamman a shiyyar Kwara ta Arewa.

“Hanyar Kishi-Kaiama na da matukar muhimmanci ga daukacin kasar saboda yawan cinikin amfanin gona ga al’ummar yankin,” in ji shi.

Gwamnan ya ce tuni gwamnatin sa ta fara aikin titin kafin ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta nemi ta dakatar da aikin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here