Dalilan dasuka sa na ki amsar mukami a Kwamitin yakin neman zaben PDP – Sam Amadi

Sam Amadi
Sam Amadi

Babban Darakta, na rukunin Makarantun Zamantakewa da Siyasa ta Abuja Dokta Sam Amadi ya yi watsi da nadinsa da akai masa a matsayin Daraktan Bincike na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP na 2023.

Shahararren malamin ya ce ya ki amincewa da tayin ne saboda sabanin ra’ayi, inda ya ke rike da mukamin jagoran fafutuka daban-daban.

Amadi ya bayyana haka ne a cikin wasikar da ya rubuta mai dauke da kwanan watan 10 gawatan Oktoba 2022, zuwa ga Darakta-Janar na Kwamitin kuma Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Tambuwal mai taken, ‘Rashin amincewa da nada shi a matsayin Daraktan Bincike na Jam’iyyar PDP.

“Na farko, ina godiya da tayin zama daraktan bincike na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023. Ina ganin babban abin alfahari ne a yi la’akari da cewa ya dace da irin wannan babban mukami na babban kwamitin shugaban kasa. .

“Nagode matuka, ba zan iya karɓar tayin da akaimin na nadin ba.

“Rashin amincewa da tayin da akayimin, ba yana nufin banida bada lamuni ga Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDPn bane ko kuma kin amincewa da kyawawan halaye na ‘ya’yan waccan babbar jam’iyya da dan takararta na shugaban kasa.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here