Hadarin Kwale Kwale: Adadin Wadanda Suka Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwan Da Ya Afku A Jihar Anambra Ya Kai 76

E82C7675 9944 4B6A 99EA E95C51692429 w1023 r1 s
E82C7675 9944 4B6A 99EA E95C51692429 w1023 r1 s

Adadin wadanda suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya ya karu zuwa 76, in ji shugaba Buhari.

Jirgin ruwan ya kife ne a ranar Juma’ar da ta gabata, sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a yankin Ogbaru da ke Anambra, kamar yadda jami’ai suka bayyana a ranar Asabar, inda suka ce akalla mutane 10 ne suka mutu yayin da wasu 60 suka bace.

A wata sanarwa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, ya ce hukumomin gaggawa sun tabbatar da adadin wadanda suka mutu ya karu.

Hukumomin kasar na kokarin ceto duk wani fasinja da ya bata, in ji Buhari, ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa da su duba ka’idoji don hana afkuwar hadurra a nan gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here