Iya wannan dandazon jama’ar ya nuna ana bukatar sabon Shugabanci – Kwankwaso

IMG 20221009 154206 scaled 1
IMG 20221009 154206 scaled 1

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce dimbin jama’ar da suka tarbe shi yau a Kano na nuna karara yadda suke tsananin kwadayin samun sabon shugabanni a Najeriya.

Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wurin kaddamar da ofishin yakin neman zaben na Jam’iyar NNPP na jihar Kano, a yammacin Lahadi.

Ya ce jam’iyyar NNPP na shirin lashe zaben shugaban kasa a 2023 da manya-manyan madafun siyasa a Najeriya.

“Wannan taron dandazon jama’a yana nuna yadda mutane ke bukatuwar neman sabon shugabanci, ba a jihar kadai ba, har ma da kasa baki daya.

“Ina sanar muku cewa babban abin mamaki nan gaba kadan zai zo lokacin da jam’iyyarmu ta NNPP zata lashe zaben shugaban kasa a 2023 in Allah Ya yarda.

Kwankwaso ya ci gaba da cewa, jam’iyyar ta shirya tsaf dan lashe zabe a Kano da Najeriya, inda ya bayyana jam’iyyar NNPP a matsayin jam’iyyar siyasa wadda tayi shura tareda saurin bunkasa cikin kankanen lokaci a Afirka.

Dayake jawabi ga magoya bayansa da sukayi dandazo na taya shi murna, Kwankwaso ya ce nan da shekarar 2023 matasa za su yi murmushi su dawo hayyacin su, su koma makaranta.

“Wadanda ya kamata su yi makarantar firamare za su dawo, wadanda kuma suka kammala sakandire za mu fitar dasu jami’o’in kasashen waje.”

Tun da farko dai Dubun dubatar magoya bayan jam’iyyar da ‘yan takara da ’yan kasuwa da jiga-jigan jam’iyyar sukai cikar kwari domin sauraran jiran jagoransu Kwankwaso tareda rera sunan sa “kwankwaso” “kwankwaso” “kwankwaso”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here