Idon za’a iya tunawa dai a baya, Dubai ta tsare wasu ‘yan Najeriya a Filin tashi da saukar jiragen sama na kasar, tare da kwace shaidar sahalewar su na shiga.
“Abinda Dubai sukai shine, sun kara tsaurara hanyoyin da ake bi wajan samun damar shiga kasar, duk wanda yake kasa da shekara 30 ba zai shiga kasar ba, ko dan waye kai.”
“Abi na biyu kuma shine, duk wanda yake son zuwa Dubai sai ya bada bayanan asusun sa na wata shida da suka wuce, da kuma bayanan inda mutum zai sauka idon yaje, idon kuma kayi musu karya ko ka bada bayanan karya zasu dawu da kai ne kasar ka.”
Shugaban hukumar ta NiDCOM ta bayyana hakan ne a yayin wata hira da akai da ita a gidan TV na Arise Tv.
“An hana shiga sanan kuma an dawo da su gida domin basu bi hanyar data dace ba yayin shiga”
Sannan kuma ta bawa ‘yan Najeriya shawara dasu dai na bata sunan Najeriya a idon Duniya.













































