Hukumar hasashen yanayi ta NiMet a hasashen yanayin da tayi na cikin kwanakin nan, ta hararo cewa za a yi ruwan sama mai matukar yawa a jihohi biyar na arewacin Najeriya tare da babban birnin tarayya. Jihohin da gagarumin ruwan saman zai shafa sun hada da wasu sassan jihar Kaduna, Niger, Bauchi, Filato, Nasarawa da babban birnin tarayya.
A rahoton yanayi na kwanakin nan, NiMet tace za a samu matsakaicin ruwan sama a jihohi kamar Kwara, Oyo, Kogi, Ogun, Ekiti, Ondo, Sokoto, Katsina, Zamfara, Kebbi, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Gombe, Adamawa, Taraba, Benue, Cross River, Akwa Ibom, Ebonyi, Enugu, Abia, Imo, Anambra, Rivers, Edo da Delta.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, ana tsammanin za a samu ruwan sama mara yawa suka matsakaici a wasu sassan kasar nan cikin kwanakin.
“Yayin da za a samu kadan ko kuma babu ruwan saman a wasu tsirarun jihohi. A sakamakon ruwan mai yawa a wasu jihohin, za a iya samun ambaliyar ruwa a tituna, rafuna da gidajen dake kwari.”
“Hakazalika, ana tsammanin matsakaicin ruwan saman zai taho da iska mai karfi ballantana a jihohin arewacin Najeriya da tsakiyar kasar a cikin kwanakin.”
“Don haka ana shawartar jama’a da su kiyayi kwari , kada a yi tukin cikin ruwa, hanyoyin ruwa, a gujewa kasan bishiyoyi da duk wani wurin da bashi da tabbas a yayin ruwan kuma a kashe kayayyakin wutar lantarki kafin a fara ruwan saman,” ya kara da cewa.”













































