Ministar ma’aikatar bada Agaji da jin kan Jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta jaddada kudirinta na tabbatar da nasarar aiwatar da shirye-shiryen bada agaji na Gwamnatin Buhari da nufin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekarar 2030.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata ta hannun mai ba ta shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Nneka Ikem Anibeze, ministar ta bayyana cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba.
Ta jaddada cewa ministar ba ta taba karkatar da wani abu na shirin da ake yi wa jihohi 36 da babban birnin Tarayya zuwa Bauchi ba, bisa zargin da wasu ke na cewa tana Karkarar da wasu shirye-shiryen zuwa Bauch kuwai saboda alakarta da Jihar.
Sanarwar ta kuma tunatar da cewa, tun lokacin da aka kafa ma’aikatar a shekarar 2019 akalla mutane miliyan 20 ne suka ci gajiyar shirye-shirye da tsare-tsare daban-daban da suka hada da matasa Miliyan 1 da dubu 64 da 774 da suka kammala karatu da wadanda ba su kammala karatunsu ba a karkashin shirin NPower wanda jihar Bauchi ta kasance ta 11 a cikin jihohi 36.
A karkashin shirin ciyar da makarantun Firamare kuwa yara miliyan 9 da Dubu 900 Yan aji 1 zuwa 3 dake karatu a makarantun gwamnati dubu 53,000 a fadin kasar a halin yanzu suna samun abinci mai gina jiji a dukkan ranakun makaranta kuma jihar Bauchi ita ce ta hudu a jerin jihohin dake da yawan makarantun firamare.
Sanarwar ta bayyana cewa, ministar ta tafi kasar Saudiyya ne domin gudanar da ayyukanta na addini tare da iznin shugaba Buhari nan take bayan ta ba da tallafin kudi ga kungiyoyi masu bukata ta musamman a Oshogbo, ba Bauchi ba, kuma ana sa ran dawowarta a cikin makon nan.
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, matakin da ma’aikatar ta dauka ya zama dole ne ta hanyar daidaita al’amura a daidai lokacin da talakawa da marasa galihu da aka samar da ma’aikatar saboda dasu ke ci gaba da nuna farin cikin su da irin jagoranci nagari da ministan ta yi wajen rage radadin talauci a kasar nan ta hanyar shirye-shirye da tsare-tsare daban-daban a karkashin gwamnatin Buhari, wato “Ajandar fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci”.












































