IMF ta shawarci babban bakin Najeriya, CBN, da ya tsawaita wa’adin daina karɓar tsoffin kuɗi

old naira notes
old naira notes

Hukumar bada lamuni ta duniya (IMF), ta shawarci babban bakin Najeriya (CBN) da ya tsawaita wa’adin daina karbar tsoffin kudi, idon har karancin samun sabbin kudin ya cigaba tsamari.

Wakilin hukumar a Najeriya, Ari Aisen, ya bada shawarar ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Tun da fari, wa’adin da babban banikin Najeriya ya bayar, shine 31 ga watan Junairu shekarar 2023, sanan kuma yakara wa’adin da kwana goma.

 

Dukka da kara wa’adin da CBN ya yi, yan Najeriya na shan wahala wajan samun sabbin kudin, wanda hakan ya jawo zan-zanga a wasu sassan Najeriya.

IMF dai itace hukuma ta farko a dunyia data fitu fili domin neman tsawita wa’adin dain amfani da tsaffin kudi a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here