Shekaru da dama, dam din Watari ya kasance cibiyar kamun kifi a yankin kogin Bagwai, dake karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano.
Mutane da dama kan zuwa Garin daga kowane fanni na rayuwa don siye da siyar da kifi, don haka harkokinsu na zamantakewa da tattalin arziki suna habaka.
Sai dai abin takaici, a yanzu harkokinsu duk sun durkushe, tattalin arzikinsu ya samu koma baya sakamakon ibtila’in hadarin kwale-kwale da ake yawan samu.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ko da a cikin watan Nuwambar shekarar da ta gabata ma ta 2021 an tabbatar da mutuwar mutane 29 ciki har da daliban makarantar Islamiyya sakamakon hadarin kwale-kwale a kogin na Bagwai dake karamar hukumar Bagwai ta jihar.
Jirgin yana dauke da fasinjoji kusan 50 ciki har da yaran makarantar islamiyya da za su gudanar da wani biki.
Wani mai tukin kwale-kwalen, Abdulhamidu Musa Dan-Kifi, ya ce ya yi asarar jiragen ruwa guda shida da ya saba yin hayar kamun kifi.
A zantawarsa da wakilin Solacebase, Dan-Kifi ya koka da cewa a halin yanzu yana rayuwa ne hannu baka hannu kwarya, tun bayan faruwar lamarin.
Sai a cewarsa ya gyara hudu daga cikin kwale-kwalen da suka lalace domin ci gaba da kula da iyalansa.
“Lokacin da ibtila’in ya faru, mun yi amfani da kwale-kwalenmu wajen ceto wadanda abin ya shafa tare da nemo gawarwakin wadanda suka mutu, Kuma akasarin jiragen kwale-kwalenmu sun lalace, ko nima Shida daga cikin jiragen ruwa na sun lalace kuma na shiga tashin hankali matuka. ‘’Babu wanda ya taimake ni, duk da an ce gwamnatin jihar za ta taimaka mana, amma shiru saboda haka dole ne in gyara kwale-kwale na don sayan abinci, ”in ji shi.
Har ila yau, wani tsohon mai kamun kifi, Yunusa Aliyu ya ce a baya yakan samun akalla Naira 10,000 a kullum daga sana’ar kamun kifi kafin abubuwa su dagule. “Kafin faruwar lamarin, wannan wurin ya kasance kasuwa, kuma mutane da yawa suna zuwa su sayi kifi a wurinmu. A kullum ina samun Naira 8,000 zuwa Naira 10,000. Amma a yanzu kasuwancinmu ya gurgunce saboda ba mu da jiragen ruwa na kamun kifi”.
Wasu dattawan yankin sun nuna rashin jin dadinsu kan gazawar gwamnatin jihar Kano wajen cika alkawarin da ta dauka na chanzawa masunta kwale-kwale, tare sa samar da jiragen ruwa na zamani guda 3 da kuma bada tallafin kudi”.
Hakazalika, wani basaraken gargajiya, Malam Umaru Bagwai, ya ce gwamnatin jihar ta gaza taimakawa masunta kamar yadda ta yi alkawari a baya.
Mallam Ummaru Bagwai ya ce an gudanar da bincike bayan hatsarin kwale-kwalen wadanda galibi masunta da manoma ne. ‘’ Bayan faruwar lamarin a lokacin da gwamnan ya ziyarci yankin, ya yi musu alkawarin kudi da sauya musu kwale-kwalen amma har yanzu ba a yi musu komai ba.
Sai dai ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta cika alkawarin da ta dauka ta hanyar samar da jiragen ruwa ga al’ummar yankin.
“Na yi magana da Gwamnan kuma ya yi alkawarin cewa za a bai wa al’ummarmu jiragen ruwa na zamani, amma ba a yi komai ba, watanni 7 kenan da faruwar lamarin. Wadanda suka ba mu kwale-kwalen da ake yin aikin ceto su kansu suna korafin cewa har yanzu basu yi musu gyara ba saboda rashin kudi. Ina kira ga Gwamnatin Jihar da ta magance matsalolin da jama’a ke ciki”.
Yayin da mazauna kauyukan ke fatan, gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da madatsan ruwa ta kasa ta sake farfado da fatansu na basu gudunmuwar jirgin ruwa mai daukar fasinjoji 18.
Lokacin da wakilin Solacebase ya shiga cikin kwale-kwalen, ya lura cewa duk fasinjojin da ke tafiya a jirgin da aka ba da gudummawa daga Bagwai zuwa al’ummar Badau suna sanye da rigunan ceto a matsayin matakan tsaro idan aka samu matsala.
Baya ga haka, matukin kwale-kwalen, Abdullahi Sani ya ce mutane 18 ne kawai aka ba su izinin shiga kwale-kwalen domin kaucewa sake afkuwar bala’in da ya faru a baya da ake zargin lodin kaya ne ya haddasa.
“Hukumar ta ce jirgin ya kamata ya dauki mutane 18 ne kawai, ciki har da ni. To yanzu abin da muke yi kenan. Kuma an umurce mu da cewa kada kowa ya shiga jirgin ba tare da rigar ceto ba”.
Sai dai da yake mayar da martani kan ikirarin mazauna garin Bagwai, kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba, ya ce kwamitin da ke karkashin jagorancin kwamandan sojojin ruwa a Kano yana gudanar da aikin samar da jiragen ruwa na zamani da gwamnatin jihar ta yi alkawari.
“Batun jiragen ruwa na zamani wani kwamiti ne karkashin jagorancin kwamandan sojojin ruwa da ke Kano. Sun tattauna batun sosai tare da shawarwari. Don haka na tabbata ko ma dai batun bai wuce Gwamnatin Jiha ba. Sai dai har yanzu kwamitin bai mika rahotonsa na karshe ba.
“Mun ga yadda Gwamna da Sarkin Bichi suka mika tallafin kudi da kayan abinci na miliyoyin Naira ga iyalan wadanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su. Hatta wadanda suke aikin ceto na tabbata gwamnati ta taimaka musu,” in ji kwamishinan.
Game da halin da masunta ke ciki, Garba ya ce gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka, inda ta dora musu alhakin gano cikakkun bayanai daga karamar hukumarsu.













































