Rundunar sojojin Najeriya ta karyata labarain da yake yawo a kafufin sada zuminta na zamani cewa rundunar bata kula da walwalar jami’an ta, da kuma rashin kayan aiki.
Rundunar ta bayyana hakan a wata sanarwa da kakin rundunar Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu ya fitar, sanarwar ta ce yunkuri ake kawai a batawa rundunar suna a idon jama’a
Sanawar ta kara dacewa rundunar na iya bakin kokarin ta wajen ganin ta kyautatawa jami’anta ta, da kuma samar musu da kayan aiki na zamani don gundanar da aikin su yace ya kamata.
sanarwar ta ce daga ciki hanyoyin da rundunar ke bi wajan kyautatawa jami’anta ya hada da tsarin bada tallafin karatu ga yaran da iyayen su suka rasa rayunkansu yayin gudanar da aiki.
Sanawar ta kuma ja hankalin sojojin da su zama masu da’a kada suyi wani abu wanda zai jaifa kasarnan cikin rudani.













































