Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta rubuta wasika ga shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu, inda ta buƙaci a bai wa jami’an hukumar damar gudanar da gwajin tu’ammali da miyagun ƙwayoyi ga ƴan siyasa masu neman yin takara a zaɓen baɗi.
Shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ne ya sanar da hakan yau Laraba yayin da yake jawabi a wajen bikin karramawa na ƙungiyar na watan ukun farko wanda aka gudanar a Abuja.
Shugaban NDLEA ɗin ya ce, a lokacin da PDP da sauran jam’iyyu za su gudanar da zaɓukan fitar da gwani, zai kuma rubuta wa shugaban hukumar na ƙasa ya kuma bukaci jami’an hukumar ta NDLEA su gudanar da gwajin ga yan siyasa masu neman manyan muƙamai.
Haka kuma, Ya yi bayanin cewa gwajin ƙwayoyin ya zama dole don tabbatar da cewa ƴan siyasar da aka bai wa wasu muhimman ofisoshi ba sa yin amfani da kuɗaɗen kasafin da ake tura wa ma’aikatunsu wajen sayen kayan maye maimakon samar da ayyukan da ake bukata ga talakawa.












































