Sojojin rundunar Guards Brigade ta Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya sun ceto Misis Adonkie, matar Janar Basil Adonkie mai ritaya, sa’o’i kadan bayan da aka yi garkuwa da ita a gidanta da ke Abuja.
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta musamman da ta bai wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce an yi garkuwa da Misis Adonkie ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar 1 ga watan Satumba, lamarin da ya sa aka tura sojoji domin bin sawun masu garkuwar cikin tsari na hadin gwiwa.
A cewar rahoton, sojoji daga rundunar Guards Brigade da kuma Hedikwatar Rundunar Sojin Kasa sun bi ta rukunin gidaje na ACO Estate da Gosa, inda suka yi arangama da masu garkuwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa sojojin sun yi nasarar ceto matar a kusa da kauyen Angwan-Sabo, yayin da wata tawagar kuma ta ci gaba da bin sawun masu garkuwar da ke tserewa.
“Da misalin karfe 11:09 na safiyar ranar Laraba, sojoji daga bataliya ta 176 Guards Battalion da bataliya ta 197 Special Forces Battalion sun tare wasu mutane biyu da ake zargi da ke tserewa a kusa da kauyen Gaube da ke karamar hukumar Kuje.
“Sojojin sun kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da kundi mai dauke da harsasai na musamman guda 19 masu girman 7.62mm daga hannun wadanda ake zargin,” in ji sanarwar.
Rundunar ta Guards Brigade ta bayyana cewa tuni aka sada matar da aka ceto da iyalanta, yayin da mutane biyu da aka kama ke tsare domin tantance su.
Rahoton ya kara da cewa sojoji sun tsananta gudanar da ayyukansu a yankin domin kamo sauran mambobin kungiyar masu laifin da suka gudu, sannan ya kara da cewa karsashinsu da kwarin gwiwarsu har yanzu yana nan.











































