Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a jam’iyyar APC Murtala Sule Garo ya sanar da taya daukacin al’ummar Musulmi maza da mata musamman na jihar Kano mai albarka murnar kammala azumin watan Ramadan da kuma bikin karamar sallah.
“A dai-dai lokacin da muke gudanar da bukuwan karamar sallah kamar yadda aka saba, kada mu manta da muhimman darusan da muka koya cikin watan Ramadan wadanda suka hada da hakuri da yafiya da jin kai da taimakon juna”. A cewar Garo.
Azumin watan Ramadan kamar yadda malamai su kai ta fadarkarwa wani kebantaccen lokaci ne da kan karato da bawa zuwa ga ubangijinsa.
Manufar darusan da ke cikin wannan wata mai alfarma shi ne su ci gaba da wanzuwa cikin al’umma don samun al’umma mai inganci.
Garo ya ce “Ina kira ga al’ummar Musulmi musamman na wannan jiha da su dukufa wajen addu’o’in zaman lafiya da arziki mai dorewa”.
“Ina yiwa kowa fatan alkairi. Allah ya karbi ibadinmu ya kuma bamu lafiya da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki”. Amin.