Tinubu ya taya Sarkin Musulmi murnar cika shekaru 70 a duniya

Sultan of Sokoto visits Tinubu in Abuja 750x430

Shugaba Bola Tinubu ya taya Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta Kasa, Mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekaru 70 da haihuwa.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa shekaru 70 na rayuwar Sarkin Musulmi sun kasance shaida kan rayuwar da aka yi ta cikin hidima, hikima da mutunci.

“Kusan shekaru ashirin kana kan gadon sarautar magabatanka, ka tattare kyawawan al’adun Daular Sakkwato, wadanda suka hada da ilimi, tawali’u da kuma jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya,” in ji shi.

A cikin jinjinar tasa ga shugaban addinin, Tinunh ya ce “A yau, ina taya miliyoyin ‘yan Najeriya murnar babban tarihi ga mutum mai kima, Mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta Kasa, a ranar cikarsa shekaru 70 da haihuwa.

“Mai Alfarma, a wannan rana ina taya ka murna da dukkan al’ummarka na Sakkwato da ma makwabta, a madadin kaina, Uwargidan Shugaban Kasa Sanata Oluremi Tinubu da kuma gwamnati da jama’ar Tarayyar Najeriya.

“Shekarunka saba’in shaida ne na rayuwar da aka shafe ta wajen hidima, hikima da mutunci.

“Ka kasance mai kwantar da hankali a lokutan rudani, mai gina tsari tsakanin addinai da al’ummomi daban-daban, kuma jagoran kwarai ba ga al’ummar Musumi kadai ba, har ma da kasarmu baki daya.

“Na san ka a matsayin shugaba mai fadin gaskiya tare da tausayi, mai ba da shawarar yin hakuri ba tare da rauni ba, kuma mai fafutukar hadin kai ba tare da yin kasa a gwiwa ba kan abin da ya yi amana da shi.

“Karkashin jagorancinka, Masarautar Sakkwato ta ci gaba da inganta ilimi, tattaunawa tsakanin addinai da ayyukan jin kai. Fafutukar da kake yi na samar da zaman tare cikin lumana da ilimantar da ‘ya’ya mata da mutuncin kowane dan Najeriya yana nuna mafi kyawun dabi’unmu na bai-daya.

“A lokacin da kake da shekaru 70, ka kasance babban mutum mai kishin kasa da ba da shawara. Fadarka da ke Sakkwato ta zama mafaka ta tattaunawa, kalamanka suna da tasiri a kowane sako na wannan kasa.

“A lokacin bakin ciki, kana jajantawa. A lokacin rarrabuwar kawuna, kana hada kai. A lokacin kokanto, kana tunatar da mu game da dan adamtakarmu da kuma makomarmu ta gari a matsayin al’umma daya a karkashin inuwar Ubangiji.”

Tinubu ya ce a matsayinsa na Shugaban Kasa, yana daraja hadin gwiwar Sarkin Musulmi wajen gina kasa.

“Goyon bayan da kake bayarwa a fannin tsaro, ci gaban al’umma da kuma jin dadin rayuwar al’ummar mu na kara karfafa ginin kasarmu. Najeriya na bukatar karin hikima irin wadda kake bayarwa kyauta,” in ji shi.

Da yake ci gaba da jawabi, Shugaban kasar ya ce “A wannan muhimmiyar ranar haihuwa, ina rokon Allah da ya ci gaba da ba ka tsawon rayuwa cikin koshin lafiya, kyakkyawan tunani da kuma ci gaba da karfi. Allah ya kare ka da iyalanka, Daular Usmaniyya da kuma Najeriya. Da fatan sarautarka ta ci gaba da zama tushen albarka, shiriyawa da daukaka.

“Mai Alfarma, ina sake taya ka murna, da fatan wadannan shekaru na rayuwarka su zama mafi albarka a gare ka.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here