Tinubu ya ba da umarnin kama mutum daya, ya dakatar da manyan sakatare uku bayan binciken ICPC ya gano karin hukumar bogi

ICPC Chairman and Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin kama wani mutum mai suna George Buchi Nwabueze cikin gaggawa, sannan ya dakatar da manyan sakatarorin gwamnati uku biyo bayan gano karin wata hukumar bogi da ke aiki a cikin Sakatariyar Gwamnatin Tarayya

Wadanda abin ya shafa sun hada da M.S. Danjuma, Nadungu Gagare da kuma Richard P. Pheelangwah.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da laifuka masu alaka (ICPC), Dr. Musa Aliyu SAN, ne ya bayyana hakan ga manema labarai na Fadar Shugaban Kasa a ranar Juma’a bayan ya yi wa Shugaban Kasa bayani karo na biyu a cikin kwana biyu, bayan wata ganawa da suka yi a ranar Alhamis.

Aliyu ya ce sabon ofishin bogin da aka gano tana amfani da sunan “National Brands Development and Made-in-Nigeria Special Project Office” an ba ta ofis ba bisa ka’ida ba a cikin Sakatariyar, sabanin dokokin da ke akwai kuma ba tare da amincewar shugaban kasa ba.

Ya ce, “Bayan karin bayani da ICPC ta yi wa Shugaban Kasa kan binciken da ake yi kan hukumar bogi ta PFIPC da kuma raunin tsari a aikin gwamnati, ICPC ta gano wata hukumar bogi da ofis mai suna National Brands Development and Made-in-Nigeria Special Project Office, wanda aka ba ta ofis ba bisa ka’ida ba a cikin harabar Sakataren Gwamnatin Tarayya,” in ji Aliyu.

Ya bayyana cewa an gano wannan ofis ne yayin gudanar da bincike mai fadi na hukumar, kamar yadda Shugaba Tinubu ya umarta a baya, inda kuma bayyana cewa mai habaka wannan ofishin bogin shi ne Yariman George Buchi Nwabueze, wanda aka gano yana amfani da sunaye daban-daban na bogi.

“Hukumar bogin, National Brands Development and Made in Nigeria Special Project Office, wani George Buchi Nwabueze ne ya habaka ta, tare da hadin gwiwar wasu ma’aikata a Sakatariyar Gwamnatin Tarayya, sabanin dokokin da ke akwai kuma ba tare da amincewar Shugaban Najeriya ba.

“An gano cewa mai tallata hukumar yana amfani da wasu sunaye daban-daban guda hudu, George Nathan, George Nathan Nwabueze, Honourable George Buchi Nwabueze, Prince George Buchi Nwabueze da kuma George Nwabueze,” in ji Aliyu.

Ya bayyana cewa ICPC ta tuntubi Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya don tabbatar da muhimman bayanai game da ofishin bogin da ake bincika, kuma ta yi wa shugaban kasa cikakken bayani kan sabbin abubuwan da ke faruwa.

“Na yi wa Shugaban Kasa cikakken bayani kan wadannan sabbin abubuwa, ICPC za ta ci gaba da bincikenta kamar yadda ya kamata,” in ji shi.

Aliyu ya ce bayan gano hakan, “Shugaban Kasa ya ba da umarni kamar haka “a kama George Buchi Nwabueze cikin gaggawa, a dakatar da manyan sakatarori nan take, M.S. Danjuma, Nadungu Gagare da Richard P. Pheelangwah,” in ji shi.

Rahoton wucin gadi na ICPC, wanda aka mika wa Shugaban Kasa a ranar 6 ga watan Agusta bayan binciken kwanaki 30, ya riga ya bayyana kasancewar wasu hukumomin bogi guda biyu, FCT Investment Promotion Agency da kuma Foreign Investment Promotion Agency and Public-Private Partnership.

Hukumar National Brands Development and Made-in-Nigeria Special Project Office ita ce hukuma bogi ta hudu da aka gano bayan badakalar PFIFC tun farkon watan Afrilu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here