Zaben Osun: Rundunar ‘Yan Sanda ta gayyaci Sanata kan kalaman barazanar kisa a wani bidiyo dake yawo

Fadahunsi Senator 750x430

Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta gayyaci dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Osun ta Gabas, Sanata Francis Fadahunsi, kan zargin barazanar da ya yi wa mambobin jam’iyyar AP gabanin zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar Asabar.

Kakakin rundunar, Abiodun Ojelabi, a ranar Laraba ya tabbatar da cewa kwamishinan ‘yan sanda mai kula da zaben, Samuel Etaifo, ya aike da sammacin gayyatar dan majalisar.

Ojelabi ya ce, “kwamishinan ‘yan sanda ya gayyace Fadahunsi. Za mu fitar da sanarwa ta musamman game da hakan nan ba da dadewa ba.”

Idan zaku iya tunawa, dan majalisar da kuma dan takarar jam’iyyar APC na karanan hukumomin Ifelodun/Boripe/Odo Otin a babban zaben 2027, Francis Eniade, sun fuskanci suka mai tsanani a ranar Talata saboda yin barazana ga mambobin jam’iyyar Accord gabanin zaben gwamnan jihar na ranar Asabar mai zuwa.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta a ranar Talata, Fadahunsi, wanda ya yi magana da harshen Yarbanci, ya ce duk wani mamban jam’iyyar Accord da aka gani a garin Ilesha na jihar Osun kafin ranar Asabar da za a yi zabe, za a kashe shi.

Majiyoyi daga inda Fadahunsi ya yi wannan jawabi mai cike da ce-ce-ku-ce sun bayyana cewa dan majalisar ya yi magana ne a fadar Owa Obokun na garin Ijesaland da ke Ilesa, lokacin wata zanga-zanga da aka shirya don nuna rashin amincewa da zargin kisan mambobin jam’iyyar APC guda uku da aka yi a Ilesa ranar Talata.

Yayin da yake magana da Yarbanci, Fadahunsi ya ce, “Mutane nawa kuka gani APC ta kashe? Mun zo nan ne don mu shaida muku cewa har zuwa ranar zabe, idan muka ga wani mamban Accord a Ilesa, za mu kashe shi.”
A wani bidiyon kuma da ya yadu ranar Talata, Eniade, wanda shi ma yake jawabi a wurin taron yakin neman zabe, ya ce kada wani mamban jam’iyyar Accord ya fito zabe a karamar hukumar Odo Otin a ranar zabe.

Eniade, wanda shi ma ya yi magana da Yarbanci, ya ce, “Ina jiran wannan ne kawai kafin na yi magana. Na rantse da Allah, duk wanda ba dan APC ba ne kada ya fito ranar zabe. Idan kuka ce ba za ku saurare mu ba, mun riga mun yi muku kashedi tun da wuri. Dukkan kuri’un Odo-Otin na APC ne.

“Ku gaya wa Egbedun (Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Osun) cewa ba ni da lokacin shi. Ni ne yayansa. Jam’iyyar Accord ba za ta iya kada kuri’a ba a Odo-Otin. Ni ne na fadi haka. Zuwa ga mambobin APC, ku koma mazabunku da rumfunan zabe ku gaya musu cewa duk wanda ba dan APC ba ne kada ya fito ya kada kuri’a.”

Da yake mayar da martani kan barazanar Fadahunsi, Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, yayin da yake zantawa da manema labarai a Osogbo, ya bukaci da a kama dan majalisar, inda ya ce kalaman nasa na iya haifar da kisan kiyashi.

Gwamnan ya ce ya mika batun ga sufeton janar na ‘yan sanda, Olatunji Disu, kuma ya bukaci bincike da kama Fadahunsi, inda ya kara da cewa IGP ya tabbatar da ganin bidiyon kuma ya ba shi tabbacin daukar mataki cikin gaggawa.

“Batu na biyu yana da alaka da bidiyon da ke yawo na Sanata Francis Fadahunsi, wanda a yau ya yi kiran da a kashe shugabannin jam’iyyar Accord, magoya bayansu da iyalansu. A cikin bidiyon, Sanatan ya ma yi barazanar cewa idan ba su sami shugabannin jam’iyyar Accord ba, su kashe matansu da shuwagabanninsu.

“Wannan lamari ya wuce batun siyasa yanzu. Wannan barazana ce ga tsaron kasa da ke bukatar kulawar Shugaban Kasa ta hanyar Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro,” in ji gwamnan.

An fassara maganata ba daidai ba – Fadahunsi

Da yake mayar da martani, Fadahunsi a cikin wata sanarwa ya ce an fassara sakonsa na cikin bidiyon ba daidai ba, inda ya ce an gyara bidiyon ne don nuna shi a matsayin azzalumi.

Fadahunsi a cikin sanarwar da ya sanya wa hannu da kansa, ya ce hankalinsa ya karkata ga wani bidiyo da aka tace wanda Davido ke yadawa a TikTok da kuma Pelumi Olajengbesi a sauran shafukan sada zumunta.

Ya ce, “Na yi magana ne game da wani Rogba, wanda abokan huldarsa na kungiyar asiri suka kashe a Esa-Oke. Gwamna ya bayyana mamacin a matsayin dansa, kuma ya taba yin takaddama da wani mamban majalisar wakilai a gidan talabijin kai tsaye. Bayanina a bayyane yake, idan ba a daina kashe-kashen ba, mu ma za mu dauki fansa.

“Duk wadanda ake kashewa ‘yan Najeriya ne, kuma hakika ‘ya’ya maza da mata na al’ummomi guda ne. Na bayyana karara cewa idan aka sake kashe mambobin jam’iyyar mu, ba za mu zuba ido muna kallo ba. Za mu kare mutanenmu, koda kuwa hakan ya faru a ranar zabe.

“Abin takaici, Davido da Olajengbesi sun dauki kasa da mintuna biyu daga cikin jawabin da ya dauki kusan mintuna 24 suka rarraba shi don cimma muradun siyasa marasa amfani. A fili yake cewa ganganci ne na juyar da magana da yaudara.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here