Majalisar Koli ta Tijjaniyya ta yi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya

IMG 20260807 WA0020 768x512 1 750x430

Majalisar Koli ta Darikar Tijjaniyya ta Duniya ta yi addu’ar samun zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a Nijeriya, gami da samun lafiyar jiki da ta zuciya ga Shugaba Bola Tinubu.

Haka kuma, majalisar ta mika ta’aziyyarta ga Tinubu bisa rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, tsohon jagoran darikar Tijaniyya a Nijeriya, wanda ya riga mu gidan gaskiya a watan Nuwambar shekarar 2025.

Khalifan Tijjaniyya na duniya daga kasar Aljeriya, Sheikh Ali Bin Arabi, shi ne ya mika sakon ta’aziyyar ga shugaban na Nijeriya a Fadar Gwamnati da ke Abuja a ranar Juma’a.

Tawagar ta kunshi wakilai daga kasashen Aljeriya, Nijeriya da Senegal, wadanda ke wakiltar mambobi sama da miliyan 400 na kungiyar a fadin duniya da kuma mambobin Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi.

Sheikh Arabi ya amince da dadaddiyar dangantakar ruhi, zamantakewa da tattalin arziki da ke tsakanin Nijeriya da Aljeriya.

“Za mu ci gaba da yin addu’ar dorewar alakar soyayya da ke tsakanin Nijeriya da Aljeriya,” in ji Arabi.

A nasa bangaren, Tinubu ya gode wa tawagar bisa ziyarar ta’aziyya da kuma addu’o’in da suka yi wa Nijeriya.

“Muna kewar mahaifinmu, Sheikh Dahiru Bauchi. Ya kasance uba abin kauna kuma babban jagora.”

Tinubu ya kuma jinjina wa darikar Tijjaniyya bisa gudunmawar da take bayarwa ga Musulunci da kuma ci gaban imani a fadin Afirka da ma duniya baki daya.

“Ina mutunta ku bisa abin da kuke yi wa Musulunci a fadin Afirka da ma duniya. Allah ya ci gaba da yi muku jagora,” in ji shi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2025, yana da shekaru 98 a duniya. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here