CBN ta soke lasisin bankunan kasuwanci 46 a fadin Najeriya

CBN Governor Yemi Cardoso 750x430

Babban Bankin Kasa na (CBN), a ranar Laraba ya sanar da soke lasisin gudanarwa na wasu bankunan kasuwanci guda arba’in da shida a fadin Najeriya.

A cewar sanarwar da Mai rikon mukamin daraktar dadarwa ta Babban Bankin, Hakama Sidi-Ali ta sanya wa hannu, matakin zai fara aiki nan take.

“Babban Bankin Kasa na CBN ya soke lasisin gudanarwa na wasu bankunan kasuwanci guda 46 daga ranar 1 ga Yuli 2026, bisa ga ikonsa da ke karkashin Sashe na 12 da 13 na Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kudi (BOFIA), 2020,” in ji sanarwar da aka buga a shafin yanar gizo na CBN.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ne ya amince da soke lasisin bankunan bayan da suka gaza cika ka’idojin da ake bukata domin ci gaba da gudana a matsayin cibiyoyin kudi masu lasisi.

“A cewar umarnin, matakin soke lasisin ya zama wajibi saboda daya ko fiye daga cikin dalilai masu zuwa:
i. Rashin isassun kadarori don biyan basuka,
ii. Rufe aiki ba tare da amincewar CBN ba,
iii. Rashin aiki da daina hada-hadar kudi,
iv. Kasa fara aiki cikin watanni 12 bayan amince da lasisid
v. Kasa kiyaye mafi karancin kudaden babban jari ba tare da asara ba,” in ji bankin.

Soke lasisin wani bangare ne na kokarin CBN na ci gaba da kare kwanciyar hankalin bangaren kudi, kare masu ajiya da tabbatar da cibiyoyin da ke da lasisi sun bi dokoki da ka’idojin yanzu.

“Babban Bankin Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen inganta tsarin kudi mai aminci, karfi da juriya kuma zai ci gaba daukan matakan sa ido da ka’idoji da suka dace, idan ya cancanta, domin kiyaye amincewar jama’a a tsarin kudi na kasa,” in ji bankin.

Ga cikakken jerin bankunan kasuwancin da abin ya shafa

S/NO SUNAN MFB MATSAYI JIHA
1 Minji-Se Churchill MFB Tier 1 Rivers
2 Merchant MFB Tier 2 Abia
3 Janmaa MFB Tier 1 Kwara
4 Busu MFB Tier 2 Niger
5 Gold MFB Tier 1 Lagos
6 Zain MFB (tsohon Dawakin Tofa MFB) Tier 2 Kano
7 Bompai MFB Tier 1 Kano
8 Ajwa MFB (Tsohon Gezawa) Tier 2 Kano
9 NOW DIGITAL MFB Tier 2 Kano
10 Crystabel Microfinance Bank Tier 1 Bayelsa
11 Chanelle MFB State Lagos
12 Abia SME MFB Tier 1 Abia
13 Kamba MFB Tier 2 Kebbi
14 Iwade MFB Tier 2 Ogun
15 Winview MFB Tier 1 Abuja
16 Zuru MFB Tier 2 Kebbi
17 Minjibir MFB Tier 1 Kano
18 Shanono MFB Tier 2 Kano
19 Sumaila MFB Tier 2 Kano
20 Rimin Gado MFB Tier 2 Kano
21 Mwaghavul MFB State Plateau
22 Sycamore MFB Tier 2 Kano
23 TOFA MFB Tier 2 Kano
24 Safegate MFB Tier 1 Lagos
25 Creekline MFB Tier 2 Delta
26 Bestar MFB Tier 1 Oyo
27 Livingspring MFB Tier 1 Cross River
28 Apple MFB Tier 2 Ogun
29 Stanford MFB State Uyo (Akwa Ibom)
30 Frontline MFB Tier 2 Anambra
31 Zafec MFB Tier 2 Kaduna
32 Supreme MFB Tier 1 Lagos
33 Bejin-Doko MFB Tier 2 Niger
34 Kanopoly MFB Tier 1 Kano
35 Bellbank MFB (tsohon Tsanyawa) Tier 2 Kano
36 Yeneng MFB Tier 2 Plateau
37 Creditville MFB Tier 1 Lagos
38 MBAG MFB Tier 1 Lagos
39 STRAIGHT SAHARA MFB Tier 1 Benue
40 OURPASS MFB Tier 2 Ondo
41 VERDANT MFB Tier 1 Lagos
42 BASAWA MFB Tier 2 Kaduna
43 CASHA MFB Tier 2 Abuja
44 ESTEEM MFB Tier 2 Kano
45 ENTERPRENEUR MFB Tier 1 Lagos
46 AVANTUS MFB Tier 2 Osun

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here