Kungiyar ‘Yan Jarida Mata ta Najeriya (NAWOJ) reshen Jihar Kano, hadin gwiwa da Hadakar Kungiyoyin masu zaman kansu da ke yaki da shan miyagun kwayoyi (CONADA) da sauran kungiyoyin al’umma, a ranar a Asabar sun fito kan hanya domin bikin Ranar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Duniya ta 2026, a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a kan illolin shan miyagun kwayoyi.
An bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Shugabar NAWOJ ta Jihar Kano, Sayyida Bahijja Malam Kabara, ta sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai a Kano.
Tattakin da aka fito kan hanya, wanda ya fara daga Titin Maiduguri ya kare a Fadar Gwamnatin Jihar Kano, ya samu halartar manema labarai, masu fafutukar yaki da miyagun kwayoyi, kungiyoyin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da suka himmatu wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.
SolaceBase ta ruwaito cewa sauran kungiyoyin da suka shiga wannan tattakin sun hada da LESPADA, NACCRAN, YOSPIS, Gidauniyar Widi-Jalo, YAADAI, IYECF, TAFTA, Jam’iyyar Matan Arewa da Gidauniyar Visionary Women for Empowerment and Humanitarian Foundation VWEHF, da sauransu.
Kabara ta bayyana karuwar shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa a matsayin abin damuwa, inda ta bukaci a dauki mataki na gaggawa da hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki domin magance matsalar.
“Karuwar ta’ammali da miyagun kwayoyi, musamman a tsakanin matasa, ya kai matakin da ke tayar da hankali kuma yana bukatar daukar mataki na gaggawa da hadin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki,” in ji ta.
Ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf bisa amincewa da kafa Kwamitin Aiki na Musamman kan Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi, inda ta ce wannan mataki ya nuna kudirin gwamnatinsa na yaki da shan miyagun kwayoyi da laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi a jihar.
Kabara ta kuma taya Ambasada Maryam Hassan ta LESPADA da Hajiya Maryam Ardi Muhammad murnar nada su a cikin kwamitin, inda ta ce zabensu yabo ne ga gudunmawar da kungiyoyin al’umma ke bayarwa wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.
“Muna yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kafa Kwamitin Aiki na Musamman kan Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi. Muna kuma taya Ambasada Maryam Hassan ta LESPADA da Hajiya Maryam Ardi Muhammad murnar wannan nadi da suka cancanta a cikin kwamitin,” in ji ta.












































