FIFA za ta biya alkalin wasa Omar Artan cikakken kudin gasar cin kofin duniya duk da an hana shi shiga Amurka

Omar Artan entry 680x430

Alkalin wasan kwallon kafa dan kasar Somali Omar Artan zai karbi cikakken kudinsa na gasar cin kofin duniya duk da an hana shi shiga kasar Amurka domin yin aiki a gasar.

Artan mai shekaru 34, jami’an shige da fice na Amurka sun tsare shi tare da yi masa tambayoyi tsawon awanni 11 a filin jirgin sama na Miami a ranar Litinin kafin su sanar da shi cewa ba za a bar shi ya shiga kasar ba. An ki amincewa da fasfo din sa na diflomasiya da bizar shiga Amurka ba a karshe.

Wani jami’in gwamnatin Amurka ya ce shawarar ta samo asali ne daga zargin “alaka da wasu da ake zargi da kasancewa mambobin kungiyoyin ta’addanci.”

Artan ya ce jami’an kan iyaka sun yi masa tambaya kan wata alaka da kungiyar ‘yan ta’adda ta Al-Shabab ta Somali, zargi da ya ki amincewa da shi.

“Ina da cikakkun takardun da suka dace da komai. Ina da biza da ta dace,” in ji Artan.
“Ni kawai alkalin wasa ne da ke kokarin cimma burinsa, babban burina na rayuwa, na zo gasar cin kofin duniya.”

Bayan an hana shi shiga, an saka Artan a jirgin da ke tashi zuwa Turkiyya. Jami’an FIFA sun taimaka masa a lokacin da ya tsaya a Istanbul kafin ya koma babban birnin Somali, Mogadishu.
Majiyoyi sun shaida wa BBC Sport cewa duk da Artan ba zai shiga gasar cin kofin duniya ba, FIFA ta yi alkawarin biyan sa cikakken kudin da zai samu a gasar, duk da a sanar da alkalan wasan kudin da za su samu a gasar cin kofin duniyar ba tun da farko, biyan kudin kan zo ne bayan gasar ta kare.

Wannan koma baya bai yi lahani ga ci gaban Artan a aikin sa ba. An kara gayyatarsa alkalin wasan da ya samu lambobin yabo don ya jagorancin kara wasan UEFA Super Cup tsakanin Paris Saint-Germain da Aston Villa a Salzburg ranar 12 ga Agusta.

Bayan ya koma kasarsa, an yi masa maraba ta musamman kuma ya gode wadanda suka goyi bayan sa.

Ya gode wa mutanensa da kasarsa kuma ya riga ya mayar da hankali kan yin aiki a gasar cin kofin duniya ta 2030.

Hana Artan shiga ya biyo bayan samun shekara mafi kyau a tarihi aikin sa. An zabe shi a matsayin alkalin wasa na farko na maza na Hukumar Kallon Kafa ta Nahiyar Afirka (CAF) a 2025, ya zama alkalin Somali na farko da ya jagoranci wasan karshe na kofin kungiyoyin Afrika lokacin da ya jagoranci wasa na biyu na Karshe na Kofin Zakarun Nahiyar Afirka na 2025 tsakanin Pyramids FC da Mamelodi Sundowns.

Haka kuma ya jagoranci wasanni 3 a gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 na FIFA a Chile, ciki har da wasan matsayi na uku, kafin ya jagoranci wasanni 2 na rukuni a gasar cin kofin Afrika, bayan ya halarci gasar a shekarar da ta gabata.

Duk da ya rasa babbar damar aikin sa, matsayin Artan a kwallon kafa ta duniya na da karfi, tare da shawarar FIFA na biyan sa cikakken kudin gasar da jajanta mass bayan bakin ciki da ya samu a karshen burin sa na gasar cin kofin duniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here