Aikin Hajji, wanda ake gudanarwa shekara-shekara, kuma daya daga cikin ginshikan Musulunci guda biyar, ya fara bisa ka’ida a ranar Litinin, tare da mahajjata sama da miliyan 1.5 da suka iso Saudiyya daga ko’ina cikin duniya.
Jami’an Saudiyya sun ce yawancin masu shigowa na zuwa ne yayin da yankin ke ci gaba da kasancewa cikin tashin hankali sakamakon raunin yarjejeniyar tsagaita wuta da ke da alaka da yakin Iran da rashin tabbas na siyasar duniya baki daya.
Saleh bin Saad Al Murabba, kwamandan rundunar fasfo ta Hajji, ya ce adadin mahajjatan waje da suka iso ya zarce miliyan 1.5. Yawancin masu ibada sun bayyana jin dadinau tare da godiya bisa samu damar gudanar da aikin.
Wani maniyyaci kuma mawallafin jaridar SolaceBase ta yanar gizo, Abdullateef Abubakar Jos, ya gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa ba shi damar gudanar da wannan ibada “Ina cikin albarka da na isa Makka, ina cikin yanayi na farin ciki,” inji shi. “bazan iya bayyana irin dadin da nake ji ba ne, da gaske. Na gode wa Allah.”
Musulmi sun gudanar da sallar musamman a Ka’aba, wurin ibada mafi tsarki a Musulunci, a masallacin Harami da suka isa Makka domin fara aikin Hajjin shekarn nan, daya daga cikin ginshikan Musulunci guda biyar da dole ne kowane Musulmi mai iko ya gudanar akalla sau daya.
Haka kuma, mahajjata sun fara iso wa Mina tun daga daren Lahadi domin shirin Arafat a ranar Talata.
Tsayawa a Dutsen Arafat a ranar 9 ga Zulhijja (Ranar Arafah) shi ne ginshiki mafi muhimmanci na aikin Hajji.
Hukumar Aikin Hajji ta Kasa ta Najeriya (NAHCON) ce ta dakko mahajjatan Najeriya daga Makka zuwa Mina.












































