Zaben Fidda Gwanin APC: Dan Janar Abdulsalami ya samu tikitin majalisar wakilai ta Chanchaga

APC Flag

Adamu Abubakar, dan tsohon Shugaban Kasa Abdulsalami Abubakar, ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar APC na Dan Majalisar Wakilai na a Karamar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja.

Jami’in da ya jagoranci zaben, AbdulMumin Attahiru, ya ce Abubakar ya samu kuri’u 30,650 ya doke abokin hamayyarsa Mista Nmaa Ahmed, wanda ya samu kuri’u 1,271.

Ya kara da cewa wani dan takara, Mista Shuaibu Mairago, ya samu kuri’u 311 a zaben da aka gudanar a fadin mazabu 11 na karamar hukumar.

Sannan ya bayyana Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin, tare da ayyana shi a matsayin dan takarar APC na zaben Majalisar Wakilai na 2026.

Hakazalika, a karamar hukumar Lapai, Jami’in da ya kula da zaben, Mista Ibrahim Usman, ya sanar da cewa Alhaji Abdullahi Mahmud ya lashe zaben fidda gwanin APC da kuri’u 8,559.

Usman ya ce Mista Sadiqu Mustapha ya samu kuri’u 395, yayin da Mista Mahawiya Yusuf ya samu kuri’u 247 a zaben da aka gudanar a fadin matsabu 10 na karamar hukumar.

Sannan ya bayyana Mahmud a matsayin wanda ya lashe zaben sannan ya ayyana shi a matsayin dan takarar jam’iyyar na karamar hukumar.

Haka kuma, Farfesa Yakubu Auna ma an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC na Magama/Rijau. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here