Gwamnatin Tarayya ta ce ta kafa fiye da cibiyoyin ilimi dubu takwas a fadin kasar nan domin fadada samun ilimin manya da ilimin da ba na makaranta ba.
Darakta mai kula da Hukumar Kula da Yaki da Rashin Karatu, Ilimin Manya da Ilimin da ba na Makaranta ba (NMEC), Dr. John Edeh, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a ranar Alhamis a Abuja.
Edeh, wanda shi ma Darakta ne na Ilimi da Ci Gaba a NMEC, ya ce an rarraba cibiyoyin a fadin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ya kara da cewa an tsara cibiyoyin ne don baiwa matasa da manyan damar cike gibin ilimin, musamman wadanda suka rasa damar zuwa makaranta a baya.
A cewarsa, ana ci gaba da samar da wasu cibiyoyin karkashin Asusun Tallafawa Ilimin a Matakin Farko, don isa ga al’ummomi a yankunsu.
“Mun bude kusan cibiyoyin karatu 136 a Babban Birnin Tarayya kadai, haka kuma mun bude fiye da cibiyoyin karatu 50 a kowace jiha.
“Misali, a Ibadan, inda muke da ofis, mun bude karin cibiyoyin karatu 74.
Haka zalika, Daraktan ya ce a Owerri ma da suke ofis, sun bude karin cibiyoyin karatu 64, haka kuma a Bauchi, Gombe, Akwa-Ibom, Kastina da Nijar.
“Wadannan su ne karin cibiyoyin karatun da muka bude don kara wadanda suke da su karfi,” in ji shi.
Edeh ya lura cewa, ko da yake a yanzu cibiyoyin ba su kai dalibi miliyan daya ba, gwamnati na kara kaimi domin daukar karin dalibai 50,000 zuwa 100,000 a cikin watanni shida masu zuwa.
“Manufarmu ita ce tabbatar da cewa cikin watanni shida masu zuwa, za mu iya mayar da karin dalibai 50,000 zuwa 100,000 zuwa cibiyoyin karatun mu.
Darakta ya kara da cewa yanzu neman ilimi da horon sana’o’i a hade suke don habaka tattalin arzikin wadanda suka amfana. (NAN)












































