‘Yan sanda sun kama wanda ake zargi da yaudarar daliban Jami’ar Bayero ta hanyar zamba na aikin karbar baki a hotal

Police olopa sabo

Rundunar ‘Yan Sandan Shiya ta Daya dake Kano, ta kama wani mai suna Richard Peter mai shekaru 32 wanda ake zargi, tare da kwato wayoyi 29 da sauran kayayyaki masu alaka da zamba na samar da aikin karbar baki a hotal ga daliban Jami’ar Bayero ta Kano.

Mai Magana da Yawun ‘Yan Sandan Shiyar, DSP Abdullahi Hussaini, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, yana mai cewa an kama wanda ake zargi ne biyo bayan korafin da aka kai wa ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.

Ya ce wanda ake zargi ya yaudari wadanda abin ya shafa ne da zargin bayar da aikin karbar baki, inda ya kara da cewa ‘yan sanda sun yi gaggawar daukar mataki kan korafin.

‘Yan sanda sun ce an kai rahoton lamarin a ranar 12 ga Mayu shekarar 2026, da misalin karfe 10 na safe, lokacin da wata tawaga ta dalibai karkashin jagorancin Clementina Paul ta gabatar da korafi cewa wanda ake zargi ya yaudare su ya kuma zage su.

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargi, yana aiki tare da wata abokiyar aikinsa mai suna Faith Dauda, ya gayyaci dalibai mata 38 zuwa otal din Mairabo da ke Sabon Gari Kano, a ranar 10 ga Mayu.

Da isowar su, aka ce an umarci wadanda abin ya shafa da su canza kaya zuwa na aiki su bar kuma wayoyinsu don an fada musu ba a yarda da amfani da waya a wurin aikin da ake zaton za a yi ba.

‘Yan sanda sun bayyana cewa wanda ake zargi daga bisani ya kai dalibai wurin cin abinci na otal din, inda ya ba da umarnin akawo abinci mai tsada na Naira 6,000 ga kowace daga cikinsu kafin ya bace ba tare da ya biya kudin ba.

Bayan jiran sa’o’i da dama, wadanda abin ya shafa sun dawo dakinsu ne kawai suka gano an sace wayoyinsu da sauran kayayyakinsu.

A cewar sanarwar, masu bincike sun yi amfani da bayanan sirri da bin diddigin fasaha suka gano daya daga cikin wayoyin da aka sace a tashar mota ta Kano Line.

“Da jami’an suka isa, wanda ake zargi ya hau mota mai zuwa Legas amma an hana shi tafiya aka kama shi a Zariya, Jihar Kaduna,” in ji sanarwar, tana mai cewa an samu nasarar kwato wayoyi 29 da sauran kayayyaki.

A halin yanzu ana tsare da wanda ake zargi a Sashen Binciken Manyan Laifuka na Shiyar kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da Shi’a ta Daya, Garba Ahmed, ya yaba wa jami’an bisa abin da ya kira aikin gaggawa da ya dogara kan bayanan sirri, yana mai sake jaddada aniyar rundunar na kare ‘yan kasa daga zamba da sauran laifuffuka masu alaka.

Ya kuma shawarci jama’a da su kiyayi tayin aikin da ba a tabbatar ba, yana gargadin kada su mika kayayyakinsu ga baki, da kuma tabbatar da sahihancin masu daukar aiki da wuraren aiki kafin halartar kowace gayyata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here